10 Satumba 2025 - 16:34
Source: ABNA24
Yemen Ta Kai Hare-Hare Da Dama A Yankin Falasdinu Da Isra’ila Ta Mamaye

Sojojin saman Yaman sun kai hari a filin jirgin saman Ramon da wasu muhimman wurare guda biyu a yankin Ummul-Rashrash a kudancin Falasdinu.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Dakarun Yaman sun sanar da cewa rundunarsu bangaren makami mai linzami ta kai hari kan wasu wurare masu muhimmanci da ke kusa da sansanin Maqbo Quds da makami mai linzami na "Palestine-2".

Kakakin rundunar sojin Yaman Manjo Janar Yahya Saree ya bayyana cewa, wannan farmakin ya yi nasara kai tsaye tare da samun hadafinsa, kuma ya tilastawa sahyoniyawa tserewa zuwa matsuguni.

Ya ce sojojin saman Yaman sun kai hari a filin jirgin saman Ramon da wasu muhimman wurare guda biyu a yankin Ummul-Rashrash a kudancin Falasdinu tare da jirage marasa matuka guda uku a lokaci guda, inda suka yi nasarar afkawa inda aka ake su.

A cewar majiyoyin, Makami mai linzamin na "Palestine-2" wani makami mai linzami mai fadin kusan kilomita 2,150 da kuma gudun awan Mach 16. Wannan makami mai linzami ya na tafiyar kilomita 2,040 a cikin mintuna 11.5 kacal.

Wannan makami mai linzami mai matakai biyu mai ƙarfi zai iya shiga cikin sauƙi cikin dukkan tsarin tsaro na gwamnatin Sahayoniya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha